ABNA24 : Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, mayakan kungiyar Taliban suna ci gaba da kara nausawa zuwa birnin Kabul fadar mulkin kasar Afghanistan da nufin kwace iko da birnin.
Rahoton ya tabbatar da cewa, a ‘yan sa’o’in da suka gabata, mayakan Taliban suna a tazarar kilo mita 50 kawai daga birnin Kabul, kuma sun katse layukan wutar lantarki da suke kai wuta zuwa cikin birnin.
Mai magana da yawun kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid ya sanar a shafinsa an twitter cewa, a daren juiya Jumaa sun kwace iko da babban birnin jihar Arzugan, inda ya ce gwamnan jihar da kuma babban jami’in ‘yan sanda na jihar sun mika wuya ga Taliban.
Hakan nan kuma ya sanar da cewa a jiya sun kwace iko da jihar Zabul, kamar yadda suka kwace iko da babban barikin sojojin gwamnati wanda yake a yankin, kuma tuni dukkanin jami’an gwamnati da suka hada da sojoji da sauran jami’an tsaro da suke yankin suka mika kai ga kungiyar cikin ruwan sanyi.
Rahotanni daga kasar ta Afghanistan dai sun tabbatar da cewa, a halin yanzu manyan biranen jihohi 18 ne suke karkashin ikon Taliban daga cikin jihohi 34 da suke a kasar.
Yanzu haka wasu bayanan na cewa an kafa wasu sojoji sa kai a wasu yankuna na kasar ta Afghanistan daa ciki har da birnin Kabul, domin yin shirin yaki da mayaka kungiyar ta Taliban, wadda take samun nasara cikin sauki wajen kwace yankunan kasar, wadda Amurka da Burtaniya da sauran kasashen kungiyar NATO suka mamaye tsawon shekaru 20.
342/